Adadin Masu Cutar Coronavirus A Najeriya Ya Kai 627

Matakan da gwamnatin jihar Legas tare da cibiyar kula da dakile yaduwar cututttuka wato NCDC suka dauka na shiga gida-gida don yi wa al’umma gwaji, ya taimaka wajen kara gano masu dauke da cutar coronavirus a Najeriya.

Rahoton baya bayan nan da cibiyar NCDC ta fitar ya nuna cewa adadin masu dauke da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 627, inda a karon farko aka samu mutane 86 masu dauke da cutar a rana daya. Jihar Legas ta samu karin mutane 70, 7 a babban birnin tarayya Abuja, 3 a jihar Katsina, 3 Akwa Ibom, sai kuma jihohin Jigawa, Bauchi, da kuma Borno inda aka samu karin mutum daya-daya.

Mutane 170 sun samu lafiya a fadin kasar, yayin da mutane 21 suka mutu.

Jihar Legas da ta fi kowacce jiha yawan masu dauke da cutar coronavirus ta dauki matakan kafa cibiyoyin yin gwaji a kananan hukumomi 20 a jihar.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Babangida Jibrin.

Your browser doesn’t support HTML5

Adadin Masu Cutar Coronavirus A Najeriya Ya Kai 627