Hedikwatar rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun hallaka mayakan Boko Haram kimanin 105.
Kakakin rundunar, kanar Sagir Musa ya tabbatar wa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa wannan ya faru ne a yankin Buni Gari da ke yankin Karamar Humar Gujba a kudancin jihar Yobe.
Artabun dai ya biyo bayan bayanan sirri da sojojin suka samu cewa yan ta'addan sun durfafo Buni Gari da zummar kawo hari a garin, inda sojojin suka afka masu.
Kanar Sagir Musa ya ce “koda yake babu wani soja da ya rasa ransa amma wasu biyu sun samu raunuka kuma a halin yanzu suna samun kula a wani asibitin sojoji.”
Babban Hafsan Hafsoshin sojjin kasar, Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai, wanda a halin yanzu ya tare shiyyar arewa maso gabas, tuni ya isa yankin na Buni Gari.
Da irin wannan nasara masana tsaro na hasashen lalle idan an dage da irin wannan namijin kokari da sojoji suka fara cimmawa a cikin kwannakin nan, za a samu cigaba a yankin.
Saurarri wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum