Adadin Masu Cutar Coronavirus a Ghana Ya Kai 3,091

Rahotanni daga kasar Ghana sun bayyana cewa adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 yanzu ya kai 3,091 kuma mutum 18 sun rasa rayukansu, lamarin da ya sa wasu ke tunanin ko za a sake dawo da matakan kulle da takaita zirga-zirga kamar yadda aka dauka a baya.

Ministan kiwon lafiyar Ghana Kwaku Agyemang Manu, ya ce gwamnati ba ta da niyar yin hakan, ko da yake ta na nazarin abubuwan da ke faruwa kuma idan ya zama wajibi ta yiwu a sake dawo da dokar kullen. A cewarsa, kwararru a fannin kimiya ne ke basu shawarwari, amma tabbas Shugaban kasa zai fito ya bayyana duk wani mataki da za a dauka idan ta kama.

Da ya ke amsa tambaya game da matakan da gwamnati za ta dauka ko ta ke dauka, bayan da wani daga cikin masu larurar kwakwalwa ya kamu da coronavirus, Manu ya ce sun samar da dakin kebe wadanda ake jinya a Patang, a wurin ake jinyar mutumin.

A yayin wata ziyara da ya kai asibitin Accra dake babban birnin kasar don jinjina wa jami'an kiwon lafiyar da ke gaba-gaba wajen yaki da annobar coronavirus, Ministan ya ja kunnen jami'an dake boye kayan aikin kariya na ma'aikata. Ma'aikatan sun yi amfani da wannan damar don gode wa ministan sun kuma yi masa tambayoyi akan yanayin da suke ciki.

Manu ya bai wa ma'aikatan tabbacin cewa akwai isassun kayan aikin kariya da za su isa a kula da 'yan kasar baki daya, sai dai ya ce labarin yadda wasu ke sace kayayyakin suna sayarwa abin takaici ne wanda ya wuce abinda hankali zai dauka.

Ga karin bayani cikin sauti daga Ridwan Abbas:

Your browser doesn’t support HTML5

Adadin Masu Cutar Coronavirus a Ghana Ya Kai 3,091