A cikin sababbin alkaluman da hukumar dakile cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fitar, wasu daruruwan mutane sun sake kamuwa da cutar coronavirus.
A cewar NCDC, mutum 348 ne cutar ta sake harba, wanda hakan ya mayar da adadin masu cutar zuwa 11,166 a kasar.
Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan ma su dauke da cutar, inda yanzu ta sake samun sabbin kamuwa 163. Sai birnin tarayya Abuja da ke bin ta da wayan sabbin wadanda suka kamu da cutar 76.
Sauran jihohin sun hada Ebonyi (23), Rivers (21), Delta (8), Nasarawa (8), Niger (8), Enugu (6), Bauchi (5), Edo (5), Ekiti (5), Ondo (5), Gombe (5), Benue (4), Ogun (2), Plateau (1), Kogi (1), Anambra (1).
A cewar hukumar, a yanzu haka Najeriya na da mutane 11,166 wadanda suka kamu da cutar, yayin da mutane 3,329 suka samu lafiya, sai kuma mutane 315 da suka mutu.