Abuja-Yau take ranar Afirka Ana wannan bukin ne duk shekara domin tunawa da kuma karrama ranar da aka kafa kungiyar hada kan kasashen Afirka da aka fi sani da sunan OAU a takaice. An kafa kungiyar ranar 25 ga watan Mayu 1963.
An kafa wannan kungiyar ce da zummar habaka tattalin arziki, da kiwon lafiya, da tsaro da ci gaban al'uma. Shekaru 52 bayan kafuwarta akwai wadanda suke yaba ayyukanta da irin nasarori data samu, akwai kuma wadanda suke ganin kungiyar bata taka rawar azo a gani ba.
Masu sukar lamirin kungiyar suna bada misali da irin rigingimu na cikin gida a kasashe kamar 'yar autawar kungiyar-Sudan ta kudu, da Burundi, da Somalia, da Angola da kuma a Najeriya, inda rikicin Boko Haram ya galabaitar da arewa maso gabashin kasar. Yanzu rikicin ya shafi kasashe makwabtan Najeriya, da suka hada da Cadi, da Nijar, da kamaru.
Amma a nasa bangaren tsohon shugaban Zanzibar Amani Karumi yace gaskiya kungiyar ta taka rawar gani sosai. Yace wadansu rigingimun suna aukuwa kwatsam ba zato ba tsammani.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5