Da safiyar jiya Asabar ne dai jami’an hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta NDLE su ka dira gidan hamshakin dan jam’iyyar PDP kuma Sanata mai jiran gado, Buruji Kashamu, wanda Amurka ke nema ruwa a jallo, su ka masa kawanya.
Hukumar yaki da safarar muggan kwayoyi ta Amurka na zargin Kashamu da safara da kuma rarraba muggan kwayoyi a shekara ta 1994.
Wakilinmu na Lagos Babangida Jibrin, ya ce a sanarwar da hukumar ta NDLEA ta raba ma manema labarai, a Lagos, ta ce ana neman Kashamu ne saboda laifin da ya aikata a Amurka da kuma bukatar Amurka ta a mika ma ta shi.
To saidai mai magana da yawunsa, Mista Austin Onioko, ya zargi wani tsohon Shugaban Najeriya da dagewa wajen sa a kama Kashamu duk kuwa da amurnin kar a kama shi da kotu ta bayar.
Gobe Litini ne dai kotu za ta fara sauraren shari’a kan batun mika Basharu ga Amurka ko kuma a’a.