Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai kai ziyara jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Mai baiwa Buhari shawara kan sha’anin kafafen sada zumunta na zamani Bahsir Ahmad ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.
“Gobe (Alhamis) Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyarar kwana daya a jihar Borno, don ya duba yadda al’amuran tsaro ke gudana a arewa maso gabashi.”
Yayin wannan ziyarar, “Buhari zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar Bornon ta gudanar."
Ziyarar na zuwa ne mako guda, bayan makamanciyarta da ya kai jihar Legas da ke kudu maso yammacin kasar.
Karin bayani akan: jihar Borno, Shugaba Muhammadu Buhari, Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum, Nigeria, da Najeriya.
A watan Fabrairun 2020, shugaban na Najeriya ya kai ziyara a jihar, bayan harin da aka kai a yankin garin Auna da ya halaka mutum 30.
Yayin wani jawabi da ya yi wa al’umar jihar a ranar Talata, Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce gwamnatin tarayya ta damu da yanayin da ‘yan gudun hijira suka shiga a jihar.
“Shugaban Najeriya ya damu da halin kakanikayi da mutane suka shiga, sannan ya himmatu wajen ganin an samu zaman lafiya a Borno.”Zulum ya ce.
Daga cikin ayyukan da Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar, har da gidaje 4, 000 da aka gina don ‘yan gudun hijira daga cikin 10,000 da gwamnatin tarayya ta yi alkwarin samarwa.
“Wasu daga cikin gidajen an gina su ne a Kaleri, Dalori da sauran wurare a jihar.”In ji Zulum.