1. Buhari bai ce uffan ba dangane da kalaman batanci da aka ce Trump ya yi akan Afrika.
2. Trump bai nemi afuwa ba dangane da matsayarsa kan matakan shige da fice a Amurka.
3. Buhari ya yaba da dattakun da Trump ya nuna game da yankin zirin Korea ta Kudu da Arewa.
4. Trump na ganin akwai bukatar sauyi kan yadda za a kawar da shingayen cinikayya da Najeriya.
5. Buhari ne shugaban farko daga yankin Kudu da Sahara da ya kai ziyara fadar White House karkashin gwamnatin Trump.
6. Obama ya fasa sayarwa da Najeriya jiragen saman yaki bayan kuskuren harin sojan saman Najeriya a garin Rann, amma Trump ya amince.
7. Akwai sharuddan da za'a gindayawa Najeriya dangane da tallafin Dala Biliyan Daya da Amurka ke bata duk shekara.
8. Duk da cewa bai taba zuwa ba, amma Shugaba Trump ya ce bisa labarin da ya ke samu, Najeriya ce kasa mafi kyawu.
9. Buhari da Trump sun amince da cewa Najeriya na da matsalar cin hanci da rashawa.
10. Hoton da Buhari yake sa hannu akan rijistar fadar White House ya ja hankulan mutane da dama.