Abinda Yake Hana Mata Ruwan Nono Bayan Haihuwa

Wata uwa tana ba dan ta nono a asibiti

Wani sabon bincike na masana a kasar turai, ya bayyana cewa likitoci sun sami nasara wajen samar da isashshen nono ga mata masu shayar da yara ta wurin yin amfani da wani ruwan magani da ake kira insulin.

Wannan bincike shine na farko da ya bayyana yadda jijiyar nonon mata ke aiki da insulin warin tanada isashshen nono. Hakanan kuma binciken farko ne wanda ya nuna yadda yake wtanada nono yayinda uwa take shayarwa.

Masana da yawa sunyi bincike a wurare da dama bisan wannan sashi na kimiyya.
Bisa ga Dr. Nommsen, Idan aka duba kashi 20% na mata tsakanin shekara 20 da 44, suna da alamar cutar siga, akwai tunanin cewa zuwa kashi 20% na mata dake tasowa a kasar Amurka suna cikin hatsarin kamuwa da rashin isashshen nono domin rashin isar insulin.

Tace hanyar da ya kamata abi ta kiyayewa ce. Bisa ga cewarta, sauya irin abincin da ake ci da kuma motsa jiki sun fi aiki sosai fiye da kowacce kwayar magani. Kwararrun sun bayyana niyar ci gaba da bincike wadansu hanyoyin samar da isasshen nono domin shayar da jarirai.