Jami'an dake yaki da cutar sun ce yanzu an samu raguwar masu mutuwa sanadiyar cutar a jihar ta Neja. Yayin da yake bayani daraktan hukumar dake yaki da cutar Alhaji Baba Umaru ya ce tun daga shekarar 2009 kawo wannana shekarar ta 2013 mutane takwas ne kawai suka mutu sanadiyar kanjamau. Ya ce wadanda suka kamu da kwayar cutar kuma suna fama da cutar da zara an kawo su asibiti aka fara basu magani sai su mike su cigaba da rayuwarsu.Ya kara da cewa idan dai wadanda suna shan magani ne kuma suna zuwa asibiti babu wanda ya mutu.
Daga cikin mutane dubu dari biyar da saba'in da biyar da dari shida da casa'in da biyu da aka yi ma gwaji mutane dubu talatin da takwas da dari biyar da hamsin da biyu aka samu suna dauke da kwayar. Cikin wadanda aka samu da kwayar dubu goma sha bakwai da dari tara da arba'in da hudu su ke shan magani. Sauran basu kai inda zasu fara shan maganin ba sai an yi masu gwaji na gaba. In ji shi babban daraktan akwai jarirai talatin da shida dake dauke da kwayar HIV a babban asibitin gwamnati dake Minna. Ya ce a asibitin Bida sun ji akwai wasu jarirai da suke dauke da kwayar don haka sun tuntubi asibitin ya basu kidigdigar yaran da suke da su.
A halin yanzu hukumar dake yaki da yaduwar kwayar dake haddasa kanjamau ta dukufa wurin wayar da kawunan mutane a kasuwanni, da makarantu tare da raba kwarorar roba domin a tabbatar da dakile yaduwar cutar a jihar kafin zuwar shekarar 2015.
Mustafa Nasiru Batsari nada rahoto.