Abinda Masana Shari’a Ke Cewa Kan Murabus Din Babban Alkalin Najeriya Muhammad Tanko

  • Saleh Shehu Ashaka

Babban alkalin Alkalan Najeriya, Muhammad Tanko.

Masana shari’a na tsokaci kan murabus din babban alkalin Najeriya Jostis Muhammad Tanko da ya zo a bazata kasancewar ya na da sauran wa’adin har disambar badi.

Wasu lauyoyi kuma na nuna gara da ya dau matakin don ya kula da lafiyar sa da kuma kare martabar babbar kotun.

Lauyan mai zaman kan sa a Abuja Barista Buhari Yusuf ya ce tafiyar Jostis Muhammad Tanko a wannan yanayi ta na bisa tanadin doka ne.

Yusuf Ya kara da cewa duk da hakan ya zama ba sabam ba, don in duba yanda wanda ya maye gurbin sa Walter Onnoghen ya samu matasala har a ka tilasta shi ya yi murabus.

Shi kuma Barista Modibbo Bakari wanda ya san yawancin manyan alkalan kotun koli, ya ce a iya aikin sa shekaru 32 bai taba ganin inda alkalan su ka yi korafi kan babban alkali ba sai a kan Jostis Tanko.

Ku Duba Wannan Ma Alkalin Alkalan Najeriya Tanko Mohammed Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

Faruwar wannan mataki ya sa gwamnatin shugaba Buhari ta yi aiki da manyan alkalai 3 kama daga Onnoghen zuwa sabon babban alkali Olukayode Ariwoola.

Barista Bakari ya ce bai yi mamakin yanda murabus din Tanko ya zo a karkashin gwamnatin Buhari ba da salon mulkin ta kan bude damar zarge-zarge.

Kotun koli dai da a ke yi wa take da kotun Allah ya isa, ta kan yanke hukuncin da kan kawo cecekuce a Najeriya da in akwai ta gaba da ita za a iya daukaka kara.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Masana Shari’a Na Bayyana Ra’ayi Kan Murabus Din Babban Alkalin Najeriya Jostis Tanko