Ranar dai, rana ce da take bada dama a wayar da kai game da cutar don inganta hanyoyin gano cutar, habaka hanyoyin samun magungunan cutar, rage hadari kamuwa da cutar da yadda za a kula da cutar idan ta auku.
A wani bincike da hukumar kasa da kasa kan cutar sukari tayi tace a kalla mutum miliyan 537 'yan tsakanin shekara 20 zuwa 70 na fama da ciwon sukari, inda tayi hasashen adadin zai haura zuwa mutum miliyan 643 nan da shekarar 2030.
Wani sabon rahoton hukumar ya nuna cewa 3 cikin manya 4 na masu fama da ciwon suna rayuwa ne a kasashe masu tasowa ciki har da Najeriya.
A hirar shi da Muryar Amurka, Dr. Lawal Musa Tahir ya bayyana hatsarin dake tattare da ciwon sukari a lokacin da mai fama da cutar yayi watsi da sharrudan da likita ya gindaya masa inda yace cutar kan shafi sassan jiki kamar koda, ido, kwawalwa, zuciya, matsala wajen samun juna biyu da sauran su
Bincike ya nuna cewa, har yanzu ba a gano abinda ke haddasa ciwon suga ba, sai dai akan samu wani yanayi na halittar dan adam ko rashin motsa jiki ko cin abincin gwangwani da aka ingantashi da sinadarai ko kuma wasu cututtuka da ka iya haifar da cutar.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5