Abinda ‘Yan Najeriya Ke So Buhari Ya Fara Tunkara

Wasu magoya bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Abuja

Jama'a daga ciki da wajen Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo daga jinya ya kuma koma aiki, inda suke bayyana abinda suka fi so shugaban ya fi mayar da hankali a kai.

Bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabinsa ga ‘yan kasar mutane da dama suke ta bayyana ra'ayinsu kan abinda ya kamata ya fuskanta.

A irin muhawarorin da ake ta yi, wasu sun bayyana ra’ayinsu kan abubuwan da shugaban ya kamata ya fuskanta da suka hada da tunkarar matsalar tsaro da kuma yajin aikin da malaman jami’a ke yi.

‘Yan Najeriya da dama na da ra’ayin cewa tun bayan tafiyar Buhari jinya, harkar tsaro ta tabarbare musamman game da batun Boko Haram da kuma yawaitar satar mutane domin neman kudin fansa.

Ba ma ‘yan Najeriya kadai ba, a kasashe makwabta irinsu Jamhuriyar Nijar, jama’a da dama sun yi kira ga shugaban da ya tunkari matsalar tsaro musamman ta Boko Haram, lura da cewa wannan matsala ta shafi kasarsu.

Shugaba Buhari ya dawo Najeriya ne a ranar Asabar bayan da ya kwashe sama da watannin uku yana jinya a London kan cutar da har yanzu ba a bayyana ba.

Tun a farkon watan Mayu, Buhari ya tafi London, lamarin da ya sa wasu masu fafituka suka yi ta korafin cewa ya kamata ya dawo ko kuma ya sauka a mulki.

Saurari ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya da ke Kano da Mahmud Ibrahim Kwari ya tattaro mana a rahotonsa da kuma tsokacin da Habila Rabi’u, wani matashin dan siyasa ya yi a hirarsu da Sule Mumuni Barma a Yamai da ke Jamhuriyar Nijar:

Your browser doesn’t support HTML5

Abinda ‘Yan Najeriya Ke So Buhari Ya Fara Tunkara - 5'37"