Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Shugaban Najeriya Buhari Ya Sanar da Majalisar Dattawa Dawowarsa


ABUJA: Shugaba Buhari yana sanya hannu kan wasikar sanar da Majalisar Dattawa dawowarsa gida da kuma kama aiki
ABUJA: Shugaba Buhari yana sanya hannu kan wasikar sanar da Majalisar Dattawa dawowarsa gida da kuma kama aiki

Kamar yadda doka ta tanada Shugaban Naijeriya Muhammad Buhari ya sanar da Majalisar Dattawa dawowarsa gida

Yayinda zai bar Najeriya ranar 7 ga watan Mayu na wannan shekarar Shugaba Muhammad Buhari ya rubutawa Majalisar Dattawa wasikar sanar da ita tafiyarsa zuwa jinya a London.

A cikin wasikar ya mika ikon mulkin kasar wa mataimakinsa wanda a ranar ya zama Mukaddashin Shugaban Kasa har zuwa ranar da shugaban zai rubuta wata wasikar cewa ya dawo ya cigaba da aikinsa na shugabancin kasa.

Yau Litinin 21 ga watan Agustan shekarar 2017 Shugaba Muhammad Buhari ya cika wannan sharadin inda ya rabtaba hannu akan wasikar sanar da Majalisar cewa ya dawo daga London inda ya je jinya kuma zai kama aikinsa na shugabancin kasar.

Ranar Asabar 19 ga wannan watan, ranar da shugaban ya koma gida Najeriya yayi kwanaki 105 a London yana jinya.

A jawabinsa na yau da ya yiwa 'yan kasar ya ambato abubuwa 12 da suke da mahimmanci ga kasar da shugabancinsa wadanda zasu dauki hankalinsa.

Cikin wadannan abubuwa kuwa har da batun kasancewar Najeriya tsintsiya madaurinki daya wanda ba abun da ma za'a tsaya ana muhawara a kai ba ne. Akwai batun karfafa yaki da ta'addanci domin tabbatar da murkushe kungiyar Boko Haram da duk wani mai yunkurin tada zaune tsaye. Gwamnatinsa zata dakile rikicin Fulani makiyaya da manoma.

Yanzu sai asa ido a ga irin matakan da shugaban zai dauka akan wadannan lamura.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG