Alhaji Aminu Ado na magana ne a Abuja a taron kaddamar da wani littafi mai taken “Kwazon Yarinya ‘Yar Afirka” da ‘yar Najeriya ta asali da aka haifa a ruga, Khuraira Musa da ke zaune a Amurka ta rubuta.
“Za ka ga matasa na daukar sa’ao’i da dama su na yawo a yanar gizo ta wayoyinsu na salula, kuma akasari su kan kammala ne da gurguwar fa’ida ta samun labarun da ba na gaskiya ba.”
Sarkin wanda ya hori matan arewa su farka don bin sawun Khuraira na neman ilimi da amfani da shi don samun rayuwa mai ma’ana; ya zayyana dagewar marubuciya Chimamanda Adiche daga kudu maso gabas ya sa ta a sahun wadanda za su karbi lambar yabon kasa ta bana a Talatar nan daga shugaba Buhari.
Daga nan sarkin ya kammala da addu’ar zaman lafiya da ci gaban kasa.
Marubuciyar littafin Khuraira Musa da ta shahara wajen sana’ar kwalliya ga mata a Amurka, ta ce asalin ta marainiya ce da a ka haifa a rugar Fulani; amma hakan bai hana ta samun nasara a rayuwa ba har yau ta gina makaranta.
Ministar mata Pauline Tallen da ke cikin mahalarta taron ta ce wannan kwazo na Khuraira abin koyi ne ga matan arewa.
Matan wasu gwamnoni, malaman jami’a irin Dr.Furera Bagel da mai kare lafiyar marigayi Janar Abacha wato Manjo Hamza Almustapha, Sanata Isa Ali Ndako da sauran su na kan gaba a taron.
Saurare rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5