Abin Da 'Yan Yankin Niger Delta Ke Cewa Kan Takarar Buhari

Ziyarar Mataimakin Shugaban Kasa yankin Niger Delta domin neman sulhu

Saboda dalilai daban daban wasu daga yankin Niger Delta na ganin kamata ya yi shugaba Buhari ya je ya kula da lafiyarsa wasu kuma na ganin bai tsinanawa kasar komi ba saboa haka babu dalilin sake takara.

Bayan da shugaba Muhammad Buhari ya tabbatar cewa zai sake tsayawa neman shugabancin Najeriya a zaben shekarar 2019 mai zuwa, ra'ayin wasu daga Niger Delta na nuni da cewa basu goyi bayan hakan ba bisa ga dalilai daban daban.

Mr Alabo wani mutumin Rivers, ya ce Shugaba Buhari bai tsinana masu komi ba a tsawon shekaru ukun da ya yi yanzu yana mulki. Babu abun da ya yi wa yankin. Ya kara da cewa baya jin shugaban ya yi wani abun a zo a gani a fadin Najeriya. Alabo ya kara da cewa shugaban bai yiwa al'ummar kasar katabus ba, domin haka ba ba zasu sake zabarsa ba.

Bari dan jihar Rivers shi ma, ya yi kira ga shugaban kada ya tsaya sabili da lafiyarsa ba wai domin bai yiwa yankinsu aiki ba. Shawarsa ita ce shugaban ya koma neman lafiyar jikinsa ba ya sake tsayawa takara ba.

Shi ko Akim, yana cewa shugaba Buhari mutumin kirki ne amma mukarrabansa ke kawo koma baya. Su ne suka yi wa mulkinsa zagon kasa a duk fadin kasar. Yana da damar sake lashe zaben 2019 amma ba tare da mukarrabansa na yanzu ba.

Ita ko Tami Ebuwa, ta ce za ta zabi shugaban idan ya yi abun a zo a gani saboda jama'a na cikin mawuyacin hali yanzu. Idan ya canza tace zata zabeshi.

Ga rahoton Lamido Abubakar da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Abin Da 'Yan Yankin Niger Delta Ke Cewa Kan Takarar Buhari - 2' 57"