Gwamnatin dai ta dakatar da zirga-zirgan jirgin ne sakamokon harin da wasu yan’ ta’adda suka kai a watan Maris, wanda ya yi sanadiyar garkuwa da mutane masu yawan gaske.
Ministan harkokin sufurin Najeriya Mu’azu Jaji Sambo ya jaddada cewa gwamnatin kasar ta dauki dukkan matakan da suka dace wajen kare rayukan al’umma daga sake aukuwar abin da ya faru a baya,
Sai dai duk da wannan tabbaci da gwamnatin ta bayar hakan bai cire fargaba a zukatan wasu mutanen ba inda su ke ganin duk da matakan da gwamnati ta ce an dauka babu su ba shiga jiragen kasa ,
Toh a yayin da wasu ke nuna fargaba, wasu na ganin kariya na daga ubangiji domin su na da yakinin gwamnatin kasar ta dau darasi game da abin da ya faru a baya don haka za su ci gaba da shiga jiragen
Daya daga cikin babbar abin da ke sa mutane ke ci gaba da fargaba shi ne, ganin yadda aka shafe sama da watanin shida kafin a ceto dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5