Abin Da 'Yan Najeriya Ke Cewa Kan Rage Farashin Man Fetur

‘Yan Najeriya, musamman masu motocin haya da sauran ababen sufuri sun mayar da martani dangane da yarjejeniyar gwamnati da kungiyar kwadagon kasar akan ragin farashin litar Man fetur da Naira biyar.

A daren ranar litinin kungiyar kwadagon da wakilan gwamnatin Najeriya suka cimma matsaya akan sabon farashin.

Ministan kwadagon Najeriya Dr. Chris Ngige ya sanarwa manema labarai, kuma shugaban kungiyar kwadagon ta NLC Comrade Ayuba Wabba ya tabbatar, bangarorin biyu sun amince da cewa daga ranar litinin mai zuwa, ragin Naira biyar akan farashin man fetur zai fara aiki.

Ko me masu ababen hawa ke fadi dangane da wannan yarjejeniya. Ibrahim Sa'idu mai kaken a daidaita sahu ya ce, kungiyar kwadago ta yi kokari, amma ya kamata gwamnati ta kare rage farashin man fetur domin saukaka wa talawan kasar rayuwa.

A nasa bangaren, tsohon wakili a kwamitin zartarwa na kungiyar kwadagon Najeriya NLC, comrade Sa’idu Bello ya ce, ana famfani da kungiyar kwadago wajen cin zarafi da kaskantar da rayuwar marasa karfi a kasar.

Ya kara da cewa rage farashin mai da naira biyar ba zai canza komai ba.

Dr Lawan Habib Yahaya Masana tattalin arziki ya ce, wannan ragin yana da tasiri a sauran kayayyaki, kuma farashin ragowar kayayyaki bazai tashi ba.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Abin Da 'Yan Najeriya Ke Cewa Kan Rage Farashin Man Fetur