Tsohon gwamnan jahar Filato sanata, Joshua Dariye dai kotu ta yanke masa hukuncin zama gidan yari na shekaru goma sha hudu da wasu shekaru biyu ne a watan Yulin shekara 2018 bayan ta same shi da laifin wawure fiye da naira biliyan biyu, mallakar al’ummar jihar Filato.
Alhaji Ahmadu Maye wanda ya yi farin ciki da sakowar Dariye ya ce al’ummar yankinsa na Bokkos, suna murna har da buga ganguna.
Ga Husaini Shitu kuwa, sakin na Dariye yin karar tsaye ne ga yaki da cin hanci da rashawa da gwamnati ke yi.
Shi ko Danjuma Mabas ya ce rashin Joshua Dariye ya sanya su zama marayu a siyasar jihar Filato, amma yanzu za su yi walwala.
Barista Lawal Ishaq wani lauya mai zaman kansa ya ce majalisar kolin na da hurumin sakin duk wani dan fursuna da kwamitin da ta kafa ta ba da rahoton cewa ya yi nadamar laifin da ya aikata.
Gwamnonin biyu dai na daga cikin fursunoni dari da hamsin da tara da majalisar kolin ta kasa ta musu afuwa a ranar Alhamis.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5