Za a yi karawar ce a filin wasa na Teslim Balogun da ke birnin Legas a kudu maso yammacin Najeriyar.
Sai dai duka kungiyoyin biyu, ba sa bukatar nasarar wasan domin tuni ita Najeriya ta riga ta mallaki gurbinta a gasar, tun kafin ma ta kara da ‘yan wasan Jamhuriyar Benin a ranar Asabar.
Hakan ya faru ne saboda kasar Saliyo sun tashi canjaras a wasansu da Lesothon da za ta gamu da Najeriyar a yau.
Ita kuwa Lesothon ba ta bukatar wannan wasa, saboda ko da ta yi nasara, ba za ta samu damar mallakar gurbi a gasar ba, domin ita ce a karshen teburin wannan rukuni na L.
Malawi ce kasa ta baya-bayan da ta samu gurbin shiga gasar ta AFCON a
Sai Sudan, Ghana, Masar da Gambia, wacce wannan zai zamanto karaonta na farko da za ta je wannan gasa da kuma Zimbabwe wacce za ta je gasar a karo na uku a jere.