Rundunar sojin Najeriya ta kare matakin da ta dauka na mamayewa tare da rufe ofishin jaridar Daily Trust da ke Abuja, babban birnin kasar.
Wata sanarwa dauke da sa hannun Darektan yada labaran rundunar sojin, Brigadier Sani Usman Kukasheka, ta nuna cewa jaridar ta fitar da wasu bayanai kan wani shiri da sojojin ke yi na kai farmaki akan Boko Haram.
Sojojin na Najeriya sun ce, wallafa labarin tamkar bai wa mayakan kungiyar ta Boko Haram bayani ne kan shirye-shiryensu, wanda ka iya jefa rayuwar dakarunta cikin hadari.
“Wadannan bayanan sirri da ta wallafa, katsalandan ne ga sha’anin tsaro kamar yadda dokokin sashi na 1 da 2 na kundin dokokin sirrinta bayanai suka nuna.” In ji sanarwar. In ji sanarwar.
Kukashaka ya kara da cewa, sojojin na Najeriya, ba su da wata manufa ta yin fito-na-fito da ‘yan jarida, amma ya yi kira a gare su, da su zamanto masu kishin kasa.
“Saboda haka muna masu kira a gare su, da su kasance masu kishin kasa ta hanyar kaucewa kawo cikas ga harkokin tsaron kasa a rahotanninsu.”
Sanarwa ta kuma yi gargadin cewa, “ba za mu lamunci rubuce-rubucen da za su kasance suna nuna goyon baya ga ‘yan ta’adda ba, tare da yin zagon kasa ga cibiyoyinmu.”
A jiya Lahadi jaridar ta Daily Trust ta wallafa wani labari da ke nuna cewa dakarun na Najeriya na shirin kai wani farmaki a wani yankin jihar Borno, a yunkuri da suke na kwato wasu garuruwa da ake zargin sun fada hannun mayakan Boko Haram.
Wannan lamari ya sa sojojin Najeriya suka kai samame ofishin jaridar da ke birnin Maiduguri suka kama ma'aikatanta biyu.
Amma rahotannin baya-baya nan sun nuna cewa an sake su.
Daga baya ne kuma da misalin karfe hudu na yamman ranar Lahadi, wani gungun sojojin ya kai wani samame a ofishin jaridar da ke Abuja.
Bayanai sun yi nuni da cewa, an umurci dukkanin ma'aikatan jaridar ta Daily Trust da su fita waje tare da karbe na'urorin kwamfutocinsu.
"Wajen la'asar (hudu na yamma agogon Najeriya) sai ga sojoji sun zo nan a motocinsu da yawa, suka zagaye ofis din, suka ce ina Hamza Idris, sai aka ce musu Hamza ba ya aiki, sai suka ce a daina aiki suka fitar da kowa waje." In ji mataimakin babban Editan jaridar, Mahmud Jega.
Jega ya ce yana ganin wannan mataki na sojojin bai rasa nasaba da wani labari da jaridar ta wallafa.
“Babban labarin Daily Trust na ranar Lahadi, wanda ya nuna cewa sojoji suna nan sun taru da manyan makamai a Munguno suna kokarin kai hari su kwato garin Baga, ina tsammanin wannan labari ko kuma wancan, sune sanadin wannan.”
Jega ya kara da cewa, “ba su ce duka labarin karya ba ne, cewa suka yi, ba haka yanayin yake ba, ai yanayi daga nan zuwa minti 30 ma ya canza. Kuma mu ba jin dadinmu ba ne, a ce an samu koma-baya a yakin da ake yi a kasar Borno.
Rahotanni sun ce sojojin sun janye, kuma tuni har an bude gidan jaridar.
Saurari rahoton sanarwa da sojojin suka fitar daga wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5