Wani soja tsaron kasa da ke aiki a fadar gwamnatin Amurka ta White House, ya fadawa kwamitocin da ke binciken duba yiwuwar tsige Shugaba Donald Trump cewa, ya damu matuka, bayan da ya ji Shugaban Amurkan yana neman Ukraine ta binciki abokanan hamayyarsa na siyasa a wata tattaunawa da ya yi ta wayar tarho da shugaban Ukraine, lamarin da ya sa ya sanar da manyansa abin da ya ji.
Laftanar Kanar Alexander Vindman, wanda ya saurari tattaunawar da Trump ya yi a ranar 25 ga watan Yuli da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy, ya bayyana hakan ne, a wani shiryayyen bahasi da ya bayar a gaban kwamitocin majalisar wakilan Amurka.
"Na damu da na ji tattaunawar, domin a iya tunani na, hakan bai dace ba, a ce wata kasar waje ta binciki dan kasar Amurka, kuma na damu da abin da wannan mataki zai haifar ga goyon bayan da Amurka ta ke bai wa Ukraine." Inji Vindman.
Sai dai shugaba Trump, wanda a watan da ya gabata ya fitar da takardar bayanan tattaunawarsa da Zelenskiy, ya musanta ikrarin sojan, tun gabanin ma ya bayyana a gaban kwamitocin da ke gudanar da binciken cikin sirri.