Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP mai adawa, Atiku Abubakar, ya ce dakatar da babban jojin Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari ya yi mataki ne na yi wa mulkin dimokradiyya zagon kasa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na kasa da kasa da ya gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya.
"Yin watsi da umurnin kotu da kuma yi wa doka karan tsaye kan abin da ya shafi hakkin bil adama, ya nuna cewa gwamnatin Buhari ta gwammace ta bi son ranta." Inji Atiku.
Atiku ya kara da cewa, batun da ya kamata a yi dubi akai shi ne ba wai ko babban Alkalin ya yi laifi ba, kamata ya yi a duba ko an bi tsarin doka wajen dakatar da shi.
A cewar shi, matakin da gwamnatin shugaba Buhari ta dauka, ya kafa tarihin da ba a taba gani ba a kasar ko da ma a lokacin mulkin soja.
Yunkurin jin ta bakin bangaren gwamnatin ya cutura, amma a baya fadar gwamnatin ta Najeriya ta kare matakin dakatar da babban Alkalin, inda Ministan yada labarai, Lai Mohammed ya zargi Onnoghen da karya dokar kotun da’ar ma’aikata.
Your browser doesn’t support HTML5