A Yamal Bam Ya Fada Kan Ayarin Bukin Aure Ya Kashe Mutane 20

Wurin da aka kai hari a Yamal

Farmakin da rundunar sojojin hadin gwauiwa a karkashin jagorancin Saudiya ta kai a Yamal ya fada kan ayarin masu bikin aure ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 20 tare da jikata wasu da dama

Wani farmaki ta sama da rundunar hadin gwiwa karkashin jagorancin Saudia ta kai, ya abkawa wani bukin aure a arewacin Yamal, ya kashe akalla mutane 20 inji jami’an kiwon lafiya a jiya Litinin, yayin da wasu hotunan masu ban tsoro ko tada hankali suke yawo a kan kafafen sada zumunta na wannan mummunar harin bam, na uku irinsa da suka afkawa fararen hula a kasar Yamal tun karshen mako.


Wani babban likita Mohammed al-Sawmali yace angon da wasu mutane 45 sun samu raunuka kuma an kai su wani karamin asibiti na al-Jamhouri. Jami’an kiwon lafiya sun yi kira ga jama’a da su taimaka da jini


Wannan shine mummunar farmaki na uku a Yamal tun daga karshen mako. Wani farmaki ta sama a daren Lahadi ya fada kan wani gida a unguwar Hajja kuma ya kashe iyalan gidan su biyar, a cewar al-Nadhri


A ranar Asabar a kalla fararen hulla 20 ne aka kashe a wani farmaki da rundunar hadaka karkashin Saudia ta kai biyo bayan harin bam da jiragen yaki suka kaiwa wata bos dake dauke da mutane a ciki kusa da gudndumar Mowza da yaki ya daidaita a yammacin Yamal kusa da birnin Taiz da ya fada cikin yaki tsawon shekaru uku.

Rundunar hadin guiwar da Saudiyya take yiwa jagoranci taki tace uffan da kamfanin dillancin labarai na AP ya tuntube ta dangane da wadannan hare hare.