Shugaban kungiyar ta kiristoci reshen jihar Kano, Rabaran Adeolu Adeyemo ne ya gabatar da wannan bukata, a lokacin taron sauraron ra’ayoyin ‘yan kasa kan gyaran kundin tsarin mulki da kwamitin majalisar wakilai ya shirya, wanda ya samu jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Hon. Alhasan Ado Doguwaya.
Adeyemo ya bukaci gwamnati da ta soke duk tanade-tanaden da suka danganci kotunan musulunci a kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ya ce mabiya addinin kirista sun amince Najeriya ta ci gaba da zama ba ta bangaren wani addini ba, wato 'secular state' a turance, kamar yadda sashe na 10 na kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.
A cikin bukatun da kungiyar ta CAN reshen jihar Kano karkashin jagorancin Rabaran Adeyemo ta gabatar, ta ce idan gwamnati ba za ta rushe kotunan Musulunci ba, to a gyara kundin tsarin mulkin kasar don a samar da kotunan Ikilisiya wato na mabiya addinin Kirista domin yin adalci ga kowane bangare a Najeriya.
Rabaran Adeyemo ya ce idan gwamnati ta gyara kundin tsarin mulkin kasar har ya kai ga aka samar da kotunan ikilisiya, to su ma za su rika amfani ne da dokokin addinin kirista wajen gudanar da shari’a da yanke hukunci ga mabiyansu.
Haka kuma, shugaban na CAN reshen jihar Kano din ya mika bukatar tabbatar da adalci da daidaito a bangaren rabon gado tsakanin maza da mata, da kuma baiwa mata ’yancinsu na samun ilimi da sauransu.
Sauran bukatun da kungiyar CAN ta gabatar sun hada da raba ofishin ministan shari’a da na babban lauyan gwamnati wato antoni janar na tarayya, da kuma ba bangaren shari’a ’yancin cin gashin kai a bangaren kudi.
Haka kuma ta bayyana bukatar kawar da bambanci tsakanin ’yan asalin jihhoji da mazauna, tare da samar da dokokin da za su tabbatar da hukunta masu karya dokar.
Kungiyar ta CAN ta gabatar da bukatar samar wa sarakunan gargajiya da shugabannin addini matsayi a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya domin su samu kafar sauke nauyin gyara al’umma da ya rataya a wuyansu kamar yadda ya dace.
A Najeriya dai akwai kotunan gargajiya wato customary court wanda ke sauraron lamurran masu addinin gargajiya, kotunan majistare, kotunan daukaka kara, manyan kotuna, kotunan koli da dai sauransu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.
Ya zuwa lokacin hada wannan labarin, kira ta wayar tarho da wakilinmu a jihar Kano, Mahmud Kwari, ya yi don neman karin haske game da bukatun na kungiyar CAN bai kai ga samun nasara ba.