A Nijer Masu Lalura Ta Musamman Sun Yi Addu'o'in Zaman Lafiya Albarkacin Ranarsu

Taron Nakasassu 3

A janhuriyar Nijer, masu lalura ta musamman sun yi amfani da wannan rana tasu ne wajen godiya ga Allah da kuma yin addu'o'in samun zaman lafiya a kasar da ma duniya baki daya.

A yayinda ake bukukuwan ranar nakasassu ta duniya a yau 3 ga watan disamba Kungiyoyin masu bukata ta musamman a jamhuriyar Nijer sun yi taron addu’oin a dazu da hantsi a albarkacin wannan rana don neman saukin matsalar tsaron da ake fama da ita a kasar da makwaftanta inda ‘yan ta’adda ke ci gaba da karkashe bayun Allah ba kakkautawa,

Daruruwan nakasassu maza da mata ne suka hallara a farfajiyar cibiyar gamayyar kungiyoyinsu dake n’guwar Bandabari ta nan yamai inda suka yi salla raka’a 2 kafin su cike da add’uoi a matsayin wata gudunmowa a wannan lokaci da ake faman neman mafitar matsalolin tsaron da ake fuskanta a baki dayan yankin sahel, Malan Habibou Abdoulaye shine shugaban kungiyar masu bukata ta musamman na yankin Yamai.

Hukumomi sun yaba da wannan yunkuri wanda a cewarsu abu ne da zai amfani kasa fiye da yadda ake zato inji matemakim gwamnan Yamai Abdou Wada.

Halin da ake ciki sakamakon anobar coronar da ta addabi duniya ya sa kungiyoyin nakasassu takaita bukin na bana ,a maimakon shaglugula irin na nishadi sun fitar da wata sanarwa domin tunatar da hukumomi matsalolin mutanen da ke fama da tawaya a jamhuriyar Nijer.

Alkaluman kididiga sun yi nunin cewa yawan nakasassu ya haura sama da mutun 800000 daga cikn mutane million 22 da ake da su a nan Nijer saboda haka kungiyoyin kare hakkin wadanan mutane ke kara jan hankulan hukumomi akan bukatar kara yawan kudaden tallafin nan million 50 na cfa da aka saba bayarwa a kowace shekara ta yadda zasu sami abubuwan shafewa kansu hawaye a fannoni da dama.

Saurare rahoton Suleiman Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Addu'o'in Ranar Nakasassu