A Nijar Wata Kungiya Tayi Taro Akan Matsalar Bakin Haure

Shugaban Nijar Muhammadou Issoufou

Taron ya maida hankali ne kan illolin dake tattare da hadin kan da shugabannin kasashen Afirka suke baiwa kasashen Turai wajen kawwar da matsalar bakin hauren a nasu kasashen.

Musa Cangari babban magatakardar kungiyar ya kalubali shugabannin Afirka da rabtaba hannu akan yadda zasu taimakawa kasashen Turan.

Yace sun ba kasashen Turai tabbacin zasu yi masu aiki, aikin da ba zai kai kasashen Afirka gaba ba. Injishi aikin ba zai taimakawa talakawan Afirka ba. Maimakon hakan ma aikin zai kawowa kasashen Afirka matsaloli da dama.

Kungiyar ta nuna adawarta da matakan da kasashen turai ke bukatar kasashen Afirka su dauka game da matsalar ta bakin haure. Cangari ya bada misali da kasa kamar Nijar inda kasashen Turai zasu fada mata ta hana duk wani daga yammacin Afirka shiga ko ratsawa ta kasarta saboda kada ya zarce zuwa Libiya da zummar zuwa Turai.

Cangari yace tsakanin kasashen Afirka ta Yamma akwai yarjejeniyar da ta bada dama 'yan kasashen su shiga kasashen juna ba tare da wata tsangwama ba. Yarjejeniyar ta bashi damar yawo a koina a Afirka ta Yamma. Yace su kasashen Turai suna son kasashen Yammacin Afirka su taka yarjejeniyar da suka yi tsakaninsu domin su turawa su cimma muradunsu.

Amma ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar Ibrahim Yakubu ya kare gwamnatin kasar game da batun. Yace abun da kasashen Turai ke bukata shi ne a hana wadanda suke yunkurin zuwa Turai ba kan ka'ida ba. Yace hanasu ba wai a dauresu ba, a'a a basu aikin da zai dauke masu sha'awar zuwa Turai. Bisa ga wannan shirin Nijar ta bukaci kasashen Turai su bata dalar Euro miliyan dubu domin kirkiro ayyuka da mutane zasu yi.

Ga rahoton Yusuf Abdullahi da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

A Nijar Wata Kungiya Tayi Taron Akan Matsalar Bakin Haure - 2' 54"