A Nijar An Yi Muhawara Akan Yadda 'Yan Siyasar Amurka Ke Neman Kudin Zabe

Taron mahawara kai tsaye ta acebook akan yadda 'yan takarar Amurka ke tara kudi da yadda suke kashe kudin wurin neman zabe

A yayinda lokacin zaben Amurka ke karatowa an yi wata mahawara akan yadda 'yan siyasar kasar ke fadi tashin neman kudin shiga takara da yadda masu goyon bayansu ke tara masu kudi domin su tsaya takarar

Wani masanin harkokin siyasar Amurka shi ya jagoranci mahawarar kai tsaye ta kafar Facebook yana yiwa 'yan Afirka, akasari malaman jami'o'i da dalibai da 'yan rajin kare dimokradiya bayani.

Wadanda suka saurari mutumin sun yi masa tambayoyi masu yawa akan abubuwan da suke son samun masaniya dangane da yadda 'yan takarar Amurka ke fadi tashin neman yadda jama'a zasu goyi bayansu tun daga kafa kwamitin yakin zabe na kasa har zuwa na kololuwa. Ta yaya dan takara ke samun yaddar jama'a har ta kaiga kada masa kuri'a, na cikin tambayoyin.

Masanin kimiyar siyasa Farfasa Yusuf Yahaya, malami a jami'ar Yamai na cikin wadanda suka halarci taron mahawarar. Yace ya kamata a tsaya bisa kundin tsarin mulki. A ba kundun tsarin mulkin daraja kuma zabe idan lokacinshi ya yi a yi, idan kuma ya wuce a dukufa da yin aiki.

A shirin Amurka mai goyon bayan dan takara ne zai saka kudinsa domin taimaka mashi. Ba dan takarar ba ne zai ba mai goyon bayansa kudi kamar yadda take faruwa a Afirka. Masu goyon bayan dan takara a Amurka su ne suke sa ya ci zabe domin ya yiwa kasa aiki.

Wani abun da mahalarta muhawarar suka gano shi ne banbancin tasirin da kafofin labarai a sha'anin zaben Amurka keyi saboda karfin da suke dashi domin hana magudin zabe. A zaben Amurka da wuya a yi magudi ba tare da kafofin labarai sun fallasa ba. Kafofin labarai ke hana satar kuri'u a nan Amurka.

Nahiyar Afirka na iya samun mulki kamar na Amurka amma fa sai yan kasa sun daina zama wadanda za'a iya saya da su ma shugabannin ba 'yan amshin shata ba ne ma wasu, shugabanni ne da suke son kasarsu suka kuma sadakar da kansu.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

A Nijar An Yi Muhawara Akan Yadda 'Yan Siyasar Amurka Ke Neman Kudin Zabe - 3' 34"