Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Jihohin Nijar Sun Yi Taron Fadakarwa da Ma'aikatan Gwamnati


 Gwamnonin Jihohin Nijar sunyi taro da manyan ma'aikatan gwamnatin tarayyar kasar
Gwamnonin Jihohin Nijar sunyi taro da manyan ma'aikatan gwamnatin tarayyar kasar

Ma'aikatan da aka gayyato taron sun fito ne daga fannoni daban na ayyuka, su ne suka yi taro da gwamnonin da zummar fadakar dasu akan manufar gwamnatin Shugab Muhammadou Issoufou da irin rawar da ake son su taka domin cimma muradun gwamnati

Duk ma'akatan gwamnati wakilan shugaban kasa ne da gwamnati da kasar gaba daya koina aka kaisu aiki.

Saboda haka su ma'aikatan wajibi ne su wakilci jama'a da jagorancin jama'a duk inda suke.

Taron zai nuna masu abubuwan da ake kyautata zaton zasu yi da abun da ake jira daka garesu saboda cimma alkawuran da shugaban kasa ya yiwa jama'a. Za'a fadakar dasu yadda zasu taimakawa shugaban kasa cika alkawuransa.

Maganar tsaro na cikin manyan kalubale da kasar ke fuskanta saboda haka wajibi ne tsaro ya zamo kan gaba a taron abubuwan da ma'aikatan zasu maida hankali kai.

An kira talakawa su kiyaye doka, su kuma ma'aikatan, da suka kasance wakilan gwamnati, kada su sa siyasa ko kawo banbancin siyasa a harkokin ayyukansu.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG