A wani sabon nazari da kamfanin Ipsos yayi a Najeriya, ya nuna cewa ‘yan Najeriya dake amfani da wayoyin hannu wajen cinikayya kan yanar gizo hankalinsu na ‘kara kwanciya, suna sakin jikinsu wajen sayayyar a gida da kasashen waje.
Binciken ya nuna cewa ‘yan Najeriya dake amfani da wayoyi wajen sayayya sun haura na kowacce ‘kasa nahiyar Afirka baki daya, itace kuma tazo ‘kasa ta uku wadda ke da girman kasuwar wayoyi zamani a binciken da aka gudanar.
Yawan masu sayayya kan yanar gizo ya wuce kashi 47 cikin 100 na mizanin wadanda ke cinikayya a duniya, amma cikin kasashe 29 da aka gudanar da zaben jin ra’ayin mutane.
Kasar China da Indiya sune ke jagorantar kasuwar da kaso 86 cikin 100 da kaso 82 cikin 100, a bangaren yin cinikayya ta wayar hannu.
Kamar yadda binciken ya nuna yawancin mutane na amfani wayoyin zamani ne wajen yin sayayya a gida Najeriya da sauran kasashe.
Your browser doesn’t support HTML5