A Najeriya Kungiyoyin Fafutukar Kare Hakkin Yara Na Kara Samun Nasara

Kotu A Jihar Sakkwato

Kotu A Jihar Sakkwato

A Najeriya nasarorin da kungiyoyin fafutukar kare hakkin yara ke samu na haduwa da cikas domin wasu na yi masu zagon kasa, sai dai kuma kungiyoyin da hukumomin kare hakkin bil'adama sun ce sai sun ga abinda zai turewa buzu nadi.

Wannan na zuwa ne a lokacin da kungiyoyin fafutukar suka yi tsayin daka ganin an hukumta wata mata da ta ci zarafin diyar kishiyar ta fiye kima.

Fafutukar da hukumomi da kungiyoyin bayar da tallafi na kasashen duniya ke yi don ganin an ceto kananan yara daga fadawa nau'o'in cin zarafi dabam-daban ya kai ga wasu gwamnatocin jihohi a Najeriya sun samar tare da saka hannu ga dokokin kare ‘yancin kananan yara.

Sai dai wani abu mai kama da zagon kasa na fuskantar wannan kokarin a jihar Sokoto dake Arewa maso yammacin kasar, inda wata mata ‘yar shekaru 33 ta ci zarafin diyar kishiyarta wata yarinya ‘yar kimanin shekara 14, lamarin da ya janyo fushin masu fafutuka da suka nemi a yiwa yarinyar adalci.

Yanzu dai rundunar 'yan sandan Najeriya ta kaddamar da bincike akan wannan batun kuma ta gurfanar da wadda ake tuhuma gaban kuliya inda aka tuhumci matar da laifuka uku duk akan cin zarafi, sai dai taki aminta da su.

Lauyar da ke tsayawa yarinyar da aka ci zarafinta Barrister Rashida Muhammad tace sun ga alamun nasara a zaman kotun. Shi kuma lauyan dake kare matar Barrister Shamsu A. Dauda ya nemi kotu ta bada belinta.

Mai shara'a majistire Fatima Hassan, ta umurci a kai matar da ake tuhuma gidan gyara hali zuwa ranar 22 ga wannan watan na Disamba da za'a sake fitowa domin buda yiwuwar bayar da ita beli ko akasin haka.

Tuni dai gidauniyar bada tallafi ta matar gwamnan jihar Sokoto Mariya Tambuwal ta dauki dawainiyar kula da maganin yarinyar tare da neman ganin an yi mata adalci.

Masu lura da lamurran yau da kullum na ganin cewa yin adalci ga wannan yarinyar ne zai nuna cewa lallai dokokin da aka sakawa hannu a Sokoto da ma wasu jihohin kasar sun hau turbar ceto kananan yara daga fadawa tarkon cin zarafi wanda kasashen duniya suka kashe makudan kudade domin ganin an samu nasara.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

A Najeriya Kungiyoyin Fafutukar Kare Hakkin Yara Na Kara Samun Nasara