Shugaban hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta Najeriya JAMB, farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewar kimanin kashi 80 dake daukar jarabawar neman shiga Jami’o’i basu cancanta ba. wanda hakan ke nuna cewa daliban na shiga jami’o’in kasar ba tare da cancanta ba.
Alhaji Mohammed Abubakar, tsohon babban sakataren ma’aikatar ilimi yace ko a baya suna zargin hukumar JAMB da neman kudi, wanda yakamata ace sai an tabbatar da cancantar dalibi kafin a barshi ya dauki jarabawar. Yanzu haka akwai dalibai dake cin jarabawar har maki sama da 200 amma da zarar yaje shiga Jami’a sai aga bashi da turanci ko lissafi.
Kwararru a fannin ilimi a Najeriya, irin su mallam Ali Mai Baba na ganin musabbabin wannan matsala na faruwa ne tun daga tushe, kasancewar raunin da darasin lissafi da turanci yake da shi tun a karatun firamare har zuwa sakandare. Haka kuma kwararrun malamai a darussan lissafi da turanci na tafiya su nemi wani aikin maikamon koyarwa.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5