A daidai lokacin da ake cigaba da dakon sakamakon zaben Shugaban kasar jamhuriyar Nijar na ranar 21 ga watan Fabrairu, wanda kotun tsarin mulkin kasa za ta bayyana, lauyoyin da ke kare dan takarar adawa sun ce akwai alamu masu karfi da ke nuna yawan kuri’un da ya samu a wannan fafatawa sun haura kashi 54 daga cikin 100, a maimakon kashi 50.3 da aka yi ikirarin ya samu a can baya, sai dai magoya bayan jam’iyyar PNDS na cewa wannan zancen ‘yan matan amarya ne kawai.
A lokacin wani taron manema labarai da su ka kira, lauyoyin da ke kare dan takarar jam’iyar adawa ta RDR Canji, sun baje wani tulin takardun da ke kunshe da rahotannin karshen zaben da ya gabata, da nufin fayyace wa jama’a ayyukan asshan da suka ce an tafka a yankuna da dama, wanda kuma ka iya canza komai na sakamakon wucin gadin da ya ayyana Bazoum Mohamed a matsayin wanda ya yi nasara. A cewar Lirwana Abdourahmane, daya daga cikin lauyoyin Mahaman Ousman.
Da yake maida martani akan wannan sabuwar dambarwa, jigo a jam’iyyar PNDS Tarayya, Siradji Issaka cewa ya yi ba haka abin ya ke ba; gwaninsu ne ya yi nasara.
To sai dai lauyoyin na dan takarar ‘yan hamayya na ci gaba da kafewa akan bakarsu game da nasarar da su ke hasashen kotu na iya bai wa Mahaman Ousman bayan nazarin hujjojin da su ka zo da su.
Yunkurin jin ta bakin masana doka akan wannan dambarwar ya citura, dukkan wadanda muka tuntuba sun ce ba za su ce kala ba, domin a cewarsu magana ce da ke gaban kotu.
A karshen makon nan ne wa’adin nazarin sakamakon zaben na 21 ga watan Fabrairu ke shudewa, saboda haka nan gaba kadan kotun tsarin mulkin kasa za ta fitar da sunan wanda ya yi galaba a wannan fafatawa.
Ga ragoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma a cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5