Hukumomin kasar Iraq sunce rundunar mayakan hadin gwuiwa dake kara kaimi wurin patattakar yan kungiyar IS a kusa da birnin Mosul dake arewacin kasar, sun gano wani gabjejen kabari da aka samu akalla gawarwaki dari da aka gille musu kawuna.
WASHINGTON DC —
Rahotannin farko da aka samo jiya Litinin daga kafofin watasa labaran kasashen yammacin Turai da na Kurdawa sunce ana kyautata zaton gawarwakin duk na fararen hula ne.
Wani kakakin yan sandan kasar Iraq yace an gano gwarwakin ne a wata jami’ar koyarda dabarun noma dake wajen garin Hamman al-Alil mai tazarar kilomita 15 kudu daga birnin Mosul.
Hukumar yan sandan tace an aika kwararrun likitoci a wurin don sun binciki kisan kiyashin kuma su yi kokarin gane gawarwakin.
Yanzu dai an fi shekaru biyu tun lokacinda garin Mosul yake karkashin ikon mayakan kungiya IS kuma fararen hula da suka fice daga birnin sunce kungiyar ta IS tana ci gaba da kashe dimbin mutane a cikin birnin.