A Masar Mutane Biyu ne Zasu Nemi Shugabancin Kasa

Hafsan hafsoshin sojojin Masar, Janar Abdel Fattah el-Sissi dan takarar da ake harsashen zai lashe zabe mai zuwa.

A zaben shugaban kasa da za'a yi nan da wata daya a kasar Masar kawo yanzuyan takara biyu kacal zasu tsaya.
A Masar mutane biyu ne kacal zasu yi takarar shugabancin kasar a zaben da za a yi cikin watan gobe, ganin mutanen biyu ne suka mika takardun neman tsayawa zabe a cikar wa’adin haka jiya lahadi.

Tsohon babba hafsa a rundunar sojin kasar janar Abdel el Sissi zai kara da wani dan siyasa mai ra’ayin gurguzu Hamdeen sabahi.

Jami’ai daga hukumar zaben kasar suka ce janar Sissi ya gabatar da takardunsa tareda sa hanun mutane da suke goyon bayan kudurins a kusan su dubu metan, samada abunda doka ta tanadar da sa hanun mutane dubu ashirin da biyar. Sabahi ya mika takardunsa tareda goyon bayan mutane kimanin dubu talatin.

Hukumar zaben zata saki jerin sunaye na karshe ranar biyu ga watan gobe, a zabend a za a gudanar ranar 26 ga watan na Mayu.