Wata kotun Masar ta sallami wata ba-Amurkiya 'yar asalin Masar tare da wasu mutane 7, bayan kasancewa a daure na kusan tsawon shekaru uku saboda zargin safarar mutane ta wajen amfani da wata kungiyarta mai da'awar taimakon yaran da ke kan titin Alkhahira.
WASHINGTON D.C. - —
Babbar wadda ake tuhumar, Aya Hijazi, da mijinta da kuma wasu mutane 6 sun kasance cikin fursuna tun daya watan Mayun 2014, lokacin da 'yan sanda a birnin Alkhahira su ka kai samame kan gidauniyarta ba tare da wata takardar sammaci ba, su ka kwace kananan komfutoci da sauran na'urori.
An tuhumi mutane 7 din ne da laifin safarar mutane, da kuma lalata da yara kanana, da kuma biyan yara kudi su shiga zanga-zangar kyamar gwamnati. Kama su da aka yi ya janyo korafe-korafe daga kungiyoyin raji da dama, wadanda su ka ce zarge-zarge an kago ne kawai, kuma wani bangare ne na yadda gwamnati ke kokarin murkushe kungiyoyin sa kai.