Kamar yadda al'amarin ya ke a sauran wurare, masu satar mutane domin neman kudin fansa a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya na cin karensu babu babbaka, kama daga yankin Takum har zuwa Zing na arewacin jihar, lamarin yana kara ta’azzara.
Wannan matsalar na neman gagaran kundila, inda a yankin Lau lamarin ke neman kawo rudani a tsakanin al’ummar yankin, batun da ya kai hadakar kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, ta rubuta takardar koke ga hukumomin tsaro domin kawo dauki.
Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, a karamar hukumar Lau da ke jihar Taraba, Rev. Father Sunday Patrick, ya ce abubuwan da su ke faruwa a yankin Lau da Takum abin takaici ne, ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su dauki matakan magance wannan matsala da gaggawa domin samun zaman lafiya a yankin.
Shima a nasa tsokacin, Imam Umaru, na hadakar kungiyar majalisar Musulmi a yankin, y ace dole gwamnati ta tashi tsaye, su kuma al’umma sub a da gudumuwa domin yaki da wannan matsalar ta satar jama’a ana garkuwa da su domin neman kudin fansa.
Kakakin runduna yan sandan jihar Taraba, ASP David Misal, ya ce sun tura jami’an tsaro zuwa dajukan na yankin da abun yake faruwa, inda su ka yi nasarar kama wasu mutane da suke tuhuma da kama mutane a gurare daban-daban.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul-Aziz:
Your browser doesn’t support HTML5