A Karon Farko Donald Trump Ya Ziyarci Fadar White House

Trump da Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya gana da sabon zababben shugaba Donald Trump a fadar White House.

Obama yace ya tattaunawa ta fahimta kan batutuwa da dama da zababben shugaban Amurka Donald Trump, a ziyarar da yakai ta farko fadar shugaban kasar.

A yayin da yake magana daga ofishinsa, Obama yace abin mai muhimmanci gare shi yanzu shine ganin komai ya tafi daidai a kokarin mikawa sabon shugban mulki.

Obama yace jami'ai zasu tabbatar da cewa Trump da ministocinsa sun sami shirin da suke bukata daga ranar farkon da suka fara aiki, domin tabbatar da cewa sun kare Amurka. jami'an tattara bayanan sirri da na kula da tsaron kasa yanzu haka sun fara baiwa Donald Trump bayanan abubuwan da suke faruwa a kasa na tsaro da kuma na aikin da sojoji ke yi a waje.

Gwamnatin shugaba Obama ta shirya wani zama da ya hada da hukumomin gwamnati masu yawa domin taimaka fahimtar da sabon zababben shugaba Trump da mukarrabansa yadda harkokin gwamnati ke tafiya.