Wata mace mai suna Sara Asafu-Adjaye wata yar fafutika yar asalin Ghana tace tayi sha’awar gani shugabar Amurka mace ta farko.
Charles Eboune mai pashin baki ne a kan harkokin kasa da kasa a Kamaru, ya matukar damuwa ganin irin kwarewar Clinton a harkokin gwamnati na shekaru da dama amma duk bai bata daman derewa ga mulkin Amurka ba.
Dimbin mutane a nahiyar Afrika na ci gaba da bayyana damuwarsu ga irin sauye suayen da sukeganin Trump zai aiwatar.
Da alamar za a samu tafiyar hawainiya a harkokin hukumar kula da baki musamman wadanda zasu fito daga nahiyar Africa zuwa Amurka, inji Francis Kouame na kasar Ivory Coast. Abubuwa zasu yi tsanani sosai. Yace bai ji dadin nasarar Trump ba.
Tuni da wasu shugabannin Afrika da yan siyasa a kasashen Kenya, Afrika ta Kudu, Uganda, Tanzania, Burundi, Demokaradiya Jamhuriyar Congo, Somalia da sauransu suka aike sakonnin taya Trump murna.
Shima Malik Obama dan’uwa shugaba Obama ya aike da sakon taya murna ga Trump din, wanda ya baiwa rufa baya.