Rahoton ya bayyana yawan gangar man fetur da aka hako daga rijiyoyi daban daban da kuma yawan danyen man da aka fitar zuwa kasashen ketare.
Kiyasin ya hada da wanda matatun man fetur guda uku dake aiki aka sayar masu domin anfai da kuma sayarwa jama'a.
Wani dan majalisar dattawa daga jihar Yobe Alkali Jajere yace rahoton shi ne alamun shugabancin adali. Lamarin ya nuna shugaba Buhari ya dace ya rike ma'aikatar man fetur din domin tabbatar da adalci.
Shugaban ne ya yi kudurin gyra kasar da ma'aikatar. Saboda haka shi ne mafita. Yana iya nada karamin minista da zai dinga kai yana komowa.
Kiyasin ya nuna cewa an hako gangar danyen man fetur miliyan goma sha bakwai da digo hudu a watan bakwai na bana da isakar gas mai yawan biliyan dari biyu da ashirin da biyar a ma'aunin gas.
A watannin Yuli da Agusta an samu kudin shiga nera biliyan arba'in da bakwai da miliyan ashirin da shida.
To amma duk da cigaban da aka samu kungiyar dillalan man fetur ta kasa na kokawa.
Alhaji Abubakar Maigandi Dakin Gari mataimakin shugaban dillalan man fetur na kasa yace inda su suke zuwa sayo kaya yanzu suna kara kudin kaya sabanin abun da gwamnati tace a sayar masu.
Wasu depo na sayar da litar mai nera tamanin da biyu da sule biyar.Amma abun da gwamnati ta ce su sayar dashi nera saba'in da bakwai da sule shida. Wannan karin da suka yi ya sa yawancin dillalan man ba zasu iya zuwa su saya ba domin idan zasu sayar dashi akan nera tamanin da bakwai zasu yi hasara.
Wannan sabon babin na bayyana adadin man da aka hako da kudaden da aka sayar dashi ya nuna a fili irin almundahanan da aka dinga tafkawa can baya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5