A Kamaru Rikicin Kasar Ya Sa Wasu Ma'aikata Sun Fara Gudu

Wasu cikin motocin da rikicin yankin masu anfani da harshen Ingilishi ya rutsa dasu a Kamaru

Rikicin kasar Kamaru tsakanin gwamnatin kasar da 'yan aware na yankin dake anfani da harshen turanci sai kara ta'azzara yake saboda manyan ma'aikatun kasar sun soma asarar ma'aikatansu

Daya daga cikin manyan-manyar ma’aikatar nan da ake kira (Cameroon Development Corporation) da take ita ce ta biyu wajen Samar da aikin yi mafi yawa a kasar ta ce kila a tilasta mata rage yawan ma’aikata, domin ko da yawan su sun tsere wa fada tsakanin jami’an tsaro da ‘yan aware dake kokarin ganin an samar da gwamnatin ‘yan bangaren dake anfani da harshen turanci.

Kamar yadda wakilin wannan gidan radiyon Moki Edwin Kindezeka ya aiko daga garin Buea dake kudu maso yammacin Kamaru,

ma’aikatan kamfanin CDC da yawa sun gudu.

‘Yan awaren dake neman yancin kai, masu Magana da turanci sun kashe wani sojan Cameroon a cikin watan Afirilun da ya gabata a yankin.

Wannan harin yayi dalilin yin arangama jefi jefi wanda ya yi musabbabin tserewar dubban mutane daga kauyukan dake yankin, ciki ko har da sama da mutane dubu 2 daga cikin dubu 20 na ma’aikatar ta CDC.