Yan gudun hijirar dake zaune a wani sansani da aka tanadar musu a Mutum Biyu, sunce suna cikin mawuyacin hali na rashin ababen more rayuwa ta fuskar abinci da kuma kiwon lafiya. Sansanin dai yana kunshe ne mutane a kalla Dubu 1,691 wadanda tashe tashen hankula masu nasaba da addini da kuma kabilanci ya ‘dai ‘dai ta musamman daga Kudanci da kuma tsakiyar Jihar Taraba.
A cikin wannan sansanin ‘yan gudun hijira sunce rayuwa sai a hankali, domin sauro na takura musu da rashin wadataccen gurin kwanciya. Ko da yake sun sami ‘dan tallafi daga gwamnatin Tarayya, to amma fa sunce yanzu bukatarsu itace su koma gida domin gyara muhallansu.
Shugaban Sansanin na Mutum Biyu Amadu Saliyo, yace su dai suna wannan sansani ne domin basu da zabi, kuma yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wajen samar da hanyar da za a mayar da su garuruwansu.
To sai dai kuma gwamnatin jihar ta zargi ‘yan gudun hijirar ne da neman nokewa duk kuwa da cewa yanzu hankula sun fara kwantawa a wasu yankunan da aka samu tashin hankali.
Your browser doesn’t support HTML5