A Jihar Nasarawa Mummunar Gobara Ta Auku A Wani Gidan Man Fetur

Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tank Al-Makura

Mummunar gobara ta auku a babban birnin jihar Nasarwa wato Lafiya inda mutane da gidaje da ma'aikatu da dukiyoyi masu dimbin yawa suka salwanta sanadiyar wutar da ta taso daga inda ake saukar da kuma sayar da iskar gas

Hukumar 'yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da aukuwar wata mummunar gobara a gidan man fetur mai suna Nasin da ke babban birnin jihar, Lafiya.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ismail Usman ya ce ya zuwa yanzu ba su tabbatar da rasa rai ba sai dai an samu jikata da rasa dukiya mai dimbin yawa.

A cewar kakakin 'yan sandan yayinda gobarar ta auku tnakunan da bututun man din na fashewa saboda haka mutanen dake aiki a wurin su ne lamarin ya fi rutsawa dasu. Kawo yanzu akwai mutane sama da 36 da suke asibiti a nashi sanin.

Baicin kakakin 'yan sandan wasu ganau sun kara yin bayani. Aliyu Ilele ya ce suna gidan man da ya kama da wuta tare da gidan Garkuwan Lafiya, Malam Dahiru da gobarar ta rutsa da gidansa. A cewarsa an yi asarar rayuka da kuma dukiyoyi. Shi ma gidansa ya kone kurmus tare da motocin sayarwa da motocin da ke wucewa. Aliyu Ilele ya ce a babban asibitin jihar akwai gawar mutanen da suka mutu sun fi 30 kana wadanda suka jikata sun dara 50.

Dangane da hukumomin jihar, Malam Aliyu ya ce sun yi kokari da kawo doki tare da 'yan sanda ma.

Shi ko Muhammad Habibu ya ce wurin da ake saukar da sayar da iskar gas ne wuta ta tashi. A cewarsa mutanen dake wucewa da ba susan komi ba wuta ta hallakasu. Wuraren da ake gyaran motoci da gidajen mutane duk wuta ta lakumesu. Ya kira taimakon gwamnatocin jiha da na tarayya.

A saurari rahoton Zainab Babaji dakarin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

A Jihar Nasarawa Mummunar Gobara Ta Auku A Wani Gidan Man Fetur - 2' 35"