Babban jami'in tsaron wata karamar hukumar Jihar Florida inda wani hatsabibin yaro dan shekaru 19 yayi harbin kan mai uwa da wabi, ya lashi takobi jiya Lahadi cewar zai binciki irin rawar da hukumar 'yan sandarsa ta taka wajen maida martani ga lamarin, da kuma yadda aka kasa daukar matakin rigakafi a bayan irin alamun da aka yi ta gani game da wannan matashi makonni da dama kafin nan.
Babban baturen na 'yan sandan karamar hukumar Broward, Scott Israel, ya fadawa gidan telebijin na CNN cewa, zasu binciki dukkan matakan da 'yan sandansu suka dauka da wadanda ba su dauka ba. Sai dai kuma ya nuna fusatarsa sosai a kan wani kwararren dan sanda guda daya mai suna Scott Peterson, wanda yana kofar makarantar sakandaren ta Parkland a lokacin harbe-harben makonni biyu da suka shige, amma kuma ya ki shiga ciki domin takalar Nikolas Cruz, wanda ake zargi da bindige dalibai 14 da malamai 3.
‘’Scott Isreal yace wannan abu yasa ni nayi kasa a gwiwa na rashin shigan abokin aikin mu ciki’’ wannan sakaci da aiki ne. Isreal yace yana ganin hoton bidiyon abinda ya faru, ga Peterson a wajen makarantar lokacin da ake wannan ta'asar, sai kawai ya dakatar da shi daga aiki ba tare da albashi ba. Daga baya, Peterson yace yayi murabus.
Haka kuma yace masu bincike suna sake duba wayoyi har sau 18 da aka yi ma ofishinsu kan halayyan da wannan matashi ke nunawa makonni da dama kafin ya aikata wannan danyen aikin. Yace wadanda suka buga wayoyin sun bayyana cewa sunyi imanin cewa rike bindiga hannun wannan yaron wata babbar barazana ce.