Cikin kwanakin nan dai rayuka da dama ne suka salwanta a wasu jihohin Najeriya,sakamakon tashe tashen hankulan da ake samu da sau tari kan rikide su koma fadan kabilanci ko addini,lamarin da kan jawo asarar rayuka da kuma dukiya.
Jihar Adamawa na cikin irin wadannan jihohi,kuma don magance wannan matsalar ce ma,yasa hadakar majalisar kungiyar addinan Musulunci ta Muslim Council da kuma ta Kristocin Najeriya reshen jihar shirya wani taron sirri na gano bakin zaren samun fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan biyu.
Mallam Sahabo Magaji shi ne shugaban majalisar hadinkan Musulmi a jihar ta Muslim Council ,yace a taron nasu sun tattauna ne kan matsalolin dake tasowa yanzu,da akan danganta da addini.
To ko wane tasiri taron ke da shi wajen samar da zaman lafiya a jihar? Bishop Steven Dami Mamza shi ne shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa,CAN, reshen jihar Adamawa, yace dole jama’a su fahimci muhimmancin zaman lafiya.
Ana dai sa ran wannan taro dake zama irinsa na farko zai taimaka,wajen shawo kan banbance banbancen kabilanci da na addini a jihar.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5