A Jihar Adamawa Mata Ukku Cikin Dari Ke Mutuwa Bayan Haihuwa

Shugabannin kungiyar da ta raba kayan haihuwa ma mata masu juna biyu a Adamawa

Mata masu juna biyu dubu tamanin ake saran zasu anfana daga agajin kayan haihuwa a kananan hukumomi ashirin da daya dake jihar Adamawa.

Shugaban kungiyar kyautata jin dadin rayawa da koyar da sana’o’i don dogaro da kai mai zaman kanta Alhaji Ahmed Lawal ya bayyana haka da yake kaddamar da shirin a Fufore inda matan karkara masu juna biyu kimanin dubu takwas suka anfana da kayan haihuwa kyauta.

Rabon agajin kayan haihuwan inji shugaban kungiyar ya biyo bayan bayanai na cibiyar kula da kiwon lafiya matakin farko ke nuna a kalla mata uku daga cikin dari ke mutuwa lokacin haihuwa ko kasa da sa’o’I ashirin da hudu bayan sun sauka saboda dalilai na jahilci da talauci. Yana mai nuni da akwai mata da ke asarar ransu saboda basu da sukunin sayan reza idan nakuda ta taso.

Yayin da shi kuma shugaban cibiyar kula da kiwon lafiya matakin farko na jihar Adamawa Dr, Abdullahi Belel ya ce matsalar da ke yawan jawo mutuwar mata lokacin haihuwa shine na rashin tsabtar muhallin da matan kan haihu musamman a yankunan karkara inda ake anfani da ngwarzoma wajen karbar haihuwa.

Matsalar ta fi kamari a kananan hukumomi bakwai na arewacin jiha da rikicin Boko Haram ya tozarta rufe cibyoyin karbar haihuwa dalili ma ken an inji likita da ya sa yankunan komawa ga anfani da ngwarzoma.

Wasu mata masu juna biyu da suka anfana daga agajin kayan haihuwa Malama Lami Mohammed da Malama Maryam Abubakar sun ce dalilin wannan gudumawar zasu soma zuwa awo tare da fatan idan lokacin saukarsu ya yi zasu je asibiti mafi kusa.

Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

A Jihar Adamawa Mata Ukku Cikin Dari Ke Mutuwa Bayan Haihuwa - 2' 39"