Jami'an tsaron su kan kafa shingaye ne na duba ababen hawa to amma kuma sai su juya suna karban kudade daga hannun jama'a alatilas.
Wakilin Muryar Amurka dake jihar Adamawa ganao ne akan wannan irin mummunan halin jami'an tsaron wadanda tamkar suna yiwa jama'a kwace ne a kan hanya. Shi da wasu 'yan jarida sun bi hanya domin su tabbatar da gaskiyan koken jama'a. Shi da abokansa basu tsira ba domin an ci zarafinsu ta wajen tilasta masu su rabu da kudadensu.
Wakilinmu da abokansa sun tarad da jami'an tsaro da wasu matafiya suna cecekuce akan kudin da jami'an tsaron suka nema a hannunsu.
Wani direba yace kowace rana yana kashe kimanin nera dubu ukku wa jami'an tsaro domin ya cigaba da aikinsa na daukan fasinjoji. Yace dole ka bayar ko kuma su wulakantaka. Hatta fasinjoji ma zasu zagi direban idan bai bayar da kudi ba da sauri. Yace abun da su keyi sai su sauka su je su samesu su yi jinga akan abun da zasu bayar. Su kan yi jingar dari ukku ko hudu kafin su wuce. Haka ma idan sun dawo dole sai sun bada wani abu.
Amma sabon kwamishanan 'yansandan jihar Adamawa Musa Kimo da aka tunkareshi da abun da jami'ansa ke yi sai yace suna kokarin sauyawa wadanda suka dade wurin aiki domin samun nasarar yaki da bata gari. Ya kara da cewa shi da jami'ansa zasu yi aiki tsakainisu da Allah
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5