Idan an cigaba da hakan adadin yaran da zasu dinga kamuwa da cutar tamowa zai dinga karuwa a jihar.
Asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD tare da hadin gwuiwa gwamnatin jihar ta Adamawa sun shirya wani gangamin fadakar da kawunan iyaye mahimmancin shayarda yara nonon uwa.
Kwamishaniyar kiwon lafiya ta jihar Dr Fatima Atiku Abubakar ta ba mata shawarar shayar da jariransu nonon uwa har na tsawon watanni shida. Tace nonon uwa na kunshe da sinadiran da jarirai ke bukata domin girma. Shan nonon uwa zai ba yaro daman samun kwakwalwar da ta dace da kuma yin girma yadda ya kamata.
Akan irin abuncin da iyaye zasu ci su ba jariransu nono kwamishaniyar tace dama mutanen Adamawa sun gaji noma. Abun da zasu yi shi ne su wayar da kawunan iyaye irin abincin da zasu noma da kuma zasu ci domin shayarda jariransu.
Kwamishaniyar ta kira 'yan jarida da su taimaka wurin wayar da kawunan iyaye akan mahimmancin ba jariri nonon uwa.
Wakiliyar asusun yara na MDD da wata jami'ar kiwon lafiya ta jihar Adamawa duk sun gargadi mata akan shayar da jariransu nononsu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5