Tsohon ministan 'yansanda Adamu Waziri shi ya kira taron manema labarai a Abuja inda ya yi wasu zargi da cewa dole a yi gyara.
Yace a jiharsa ta Yobe matakan da aka shimfida bai ba 'yan Yobe damar su zabi shugabanni da suke so daga hawan farko har zuwa na tarayya ba.
Adamu Waziri ya kuma zargi tsohon ministan kudi Dr Yarima Lawal Ngama da yin kokarin saka jam'iyyar cikin aljihunsa. Yace sonshi ne ya mallaki jam'iyyar domin mai hannu da shuni ne. Yace Dr Ngama ya saye takardun zaben da za'a yi a jihar Yobe na jam'iyyarsu. Yace abun da Dr Ngama ya yi ya zo daidai da rade-radin da ake yi cewa shugaban jam'iyyar Ali Modu Sheriff ya riga ya zabi shugabanni a wasu jihohi domin ya samu galaba a zaben da za'a yi.
Adamu Waziri ya cigaba da cewa akwai abubuwan ganganci da aka yi da basu kamata ba. Idan ana son jam'iyyar ta yi tasiri a Yobe dole a sauraresu. Zaben da ake yi a Yobe ba'a farashi akan kaida ba saboda haka a rusa zaben.
Da yake mayarda martani Dr Lawal Ngama yace magudin da Adamu Waziri da Adamu Muazu suka yi ya sa jam'iyyar ta rasa gwamnati.Ya karyata zargin sayen takardun zabe a Abuja. Dangane da cewa Ali Modu Sheriff na anfani dasu ne yace babu wanda ya isa ya yi anfani dashi.
Mukaddashin kakakin jam'iyyar na kasa Barrister Abdullahi Jalo yace an nada kwamiti da zai duba zargin da Adamu Waziri ya yi. Yace dole ne a dubi zargin a kuma yi adalci.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5