A masallacin Muhammad Ghadafi nan ne hukumomin kolin Nijar suka hallara domin raya daren Maulidi.
Limamin masallacin Shaikh Ijabiri Umaru Ismail yayi takaitaccen jawabi domin kwadaitawa al'ummar musulmi falalar dake tattare da daren. Yace a daren ya kamata mutane su yawaita salati ga Manzon Allah (SAW) saboda wadanda zasu kasance kusa dashi cikin aljanna su ne wadanda suka yawaita salati.
Masallacin Shehu Sha'aibu na cikin masallatan da al'ummar musulmi maza da mata ke cuncurindo domin sauraren wa'azi da tafsirin al-Qur'ani albarkacin daren Maulidi.
Malamai sun yi anfani da damar akan jaddada mahimmancin zaman lafiya.Ustaz Ali Abdu mamba a kwamitin tsare-tsaren Maulidi na masallacin Shehu Sha'aibu yace haram ne musulmi yayi fada da musulmi haka kuma Annabi ya zauna lafiya a Medina da wadanda ba musulmi ba. Saboda haka yakamata musulmi su zauna lafiya da kowa.
A sakon da ya aikawa Musulmi akan bikin Maulidi kakakin gwamnatin Nijar Asumana Malam Isa ya ja hankalin 'yan kasar Nijar da kada su manta da barazanar tsaron da kasar ke fuskanta a sakamakon abubwan dake faruwa da kasashen dake makwaftaka dasu..
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5